Jummaʼa 9 Oktoba 2026 - 17:47
Ayatullah Mujtaba Khamene'i Ya Yaba Jarumtar Rundunar ’Yan Sanda (FARAJA)

Hauza/ Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i ya bayyana a cikin saƙon da ya aika a yayin Makon ’Yan Sanda cewa tsaro yana daga cikin manyan ni’imomin Allah, kuma tabbatar da shi a sassa daban-daban na Iran, daga manyan birane zuwa ƙananan ƙauyuka da unguwanni, da kuma daga kan iyakoki zuwa teku, filayen ƙasa da dazuzzuka, ya ta’allaka ne da jarumta da sadaukarwar jami’an Rundunar ’Yan Sanda ta Iran (FARAJA), wadda take ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tsaron ƙasar.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ga fassarar cikakken saƙon da Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i, Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Iran, ya aika a yayin Makon ’Yan Sanda:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Tsaro yana daga cikin manyan ni’imomin Allah, kuma tabbatar da shi a sassa daban-daban na Iran abar ƙauna, tun daga manyan birane zuwa ƙananan rukunin al’ummomi a ƙauyuka da unguwanni, daga sintirin tsaron kan iyakoki cikin yanayi mai wahala da yankuna masu bambancin yanayi, daga tsaunuka zuwa tekuna, daga filayen ƙasa da dazuzzuka zuwa tsakiyar ƙasar, duk wannan ya ta’allaka ne da jarumta da sadaukarwar jami’an Rundunar ’Yan Sanda ta Iran (FARAJA), masu ƙwazo da jajircewa, waɗanda suke ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tsaron ƙasa.

Wannan tsaro yana samar da yanayi mai kyau a fannoni daban-daban na zamantakewa, ɗabi’a da kwanciyar hankalin jama’a. Irin wannan hidima mai daraja, baya ga kasancewarta jihadi a tafarkin Allah, tana da gagarumin goyon bayan al’umma.

Muhimmiyar rawar da Rundunar ’Yan Sanda ta Iran take takawa a matakai daban-daban, tun daga manyan shugabanni da sassan gudanarwa har zuwa ofisoshin ’yan sanda da ƙananan sansanonin rundunar, wajen tabbatar da tsaro a shekarun baya-bayan nan, ta ƙara bayyana sosai. Alamomin wannan tasiri sun ƙara fitowa fili a yaƙe-yaƙen da aka tilasta wa Iran a karo na biyu da na uku.

Mayar da hankali da dagewar maƙiyin nan mai aikata laifuffuka, wato Amurka da Isra’ila, wajen kai hari kan matakai daban-daban na Rundunar ’Yan Sanda, tun daga manyan shugabanninta har zuwa jami’anta na ƙasa, ya ƙara fito da muhimmancin wannan hukuma fili.

Sai dai wannan yunƙuri na banza da munanan hare-haren da aka kai wa ginshiƙan tsarin doka da tsaron al’umma, waɗanda ba a taɓa samun irinsu a tarihi ba, ba su sa jami’an rundunar masu jarumta sun sassauta aikinsu ko da kaɗan ba. Har ma a tituna da cikin motoci, sun ci gaba da gudanar da ayyuka da nauyin da ke kansu kamar yadda suke yi a wuraren aikinsu da sansanoninsu.

Saboda haka, al’ummar Iran, waɗanda ake zalunta amma suke da ƙarfi da azama, suna godiya da ƙoƙari da hidimar da masu samar da tsaron ƙasa suke yi ba dare ba rana.

Haka nan, jami’an Rundunar ’Yan Sanda, waɗanda kamar Sojoji da Rundunar Kare Juyin Juya Hali suke fitowa daga cikin al’umma, za su iya ƙara tabbatar da amincewar jama’a ga wannan hukuma mai daraja ta hanyar kyawawan halaye da ke haifar da amincewa.

A wasu lokuta, mutane kan ɗauki wahala da sadaukarwar masu kare tsaro a matsayin abu na yau da kullum, ba tare da lura da irin ƙoƙarin da suke yi ba. Wannan zaluntar da ake yi musu da kuma kasancewarsu ba a san da su sosai ba, su ne abubuwan da suke ƙara musu lada a wurin Allah.

Ƙarfafa jami’an tsaro ta kowane fanni, ciki har da ƙarfafa ma’aikata, kayan aiki da tsarin fasaha, musamman inganta fasahohin zamani, kamar amfani da basirar na’ura (Artificial Intelligence) wajen nazarin bayanai ta hanyar da aka tsara, yana da muhimmiyar rawa wajen inganta inganci da sauƙaƙa gudanar da ayyukan Rundunar ’Yan Sanda.

Ina roƙon Allah Ya ɗaukaka darajojin shahidan Rundunar ’Yan Sanda masu girman matsayi, Ya azurta su da yardarSa da rahamarSa. Ina kuma miƙa godiyata ga dukkan iyalansu, ma’aikata, ma'aikatan da ke ƙarƙashin rundunar, da kuma jami’anta masu jarumta da kishin ƙasa, musamman kwamandanta mai jarumta, ƙwazo da basira, tare da yaba wa irin ƙoƙarin da yake yi.

Ina fatan, albarkacin addu’ar shugabanmu, Sahibuz Zaman (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), za su ƙara samun nasara wajen ɗaukaka tsaro, ƙarfin ƙasa da martabar Iran ta Musulunci fiye da yadda yake a yanzu.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei

16 ga Mehr, 1405 (8 ga Oktoba, 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha